An wallafa dukiyar da ministocin Faransa suka mallaka a karon farko
Mahukuntan kasar Faransa sun wallafa dukiyar da Ministoci suka mallaka a shafin intanet na gwamnatin kasar, a wani mataki na kwantar da hankalin ‘yan kasar sakamakon badakalar haraji da ta yi sanadiyar ministan kasafin kudi Jérôme Cahuzac yin murabus
Wallafawa ranar:
Ministocin dai sun bayyana arzikin da suka mallaka ne bayan cikar wa’adin da gwamnatin François Hollande ta kayyade a ranar Litinin 15 ga watan Afrilu domin kaucewa sake aukuwar barakar haraji da ta yi awon gaba da Cahuzac.
Cahuzac tuni ya amsa yana da asusun ajiya a bankin kasar Switzerland domin kada ya biya haraji da aka lankaya wa attajiran Faransa.
Da yammacin Litinin ne aka wallafa dukiyar Ministocin hadi da Firaminista Jean-Marc Ayrault.
Wata majiya tace Ministan harakokin waje Laurent Fabius shi ne attajiri daga cikinsu wanda ya mallaki kadarar kudi kimanin euro Miliyan 3.9.
Wani sakamakon bincike da aka gudanar a Faransa ya nuna kashi 63 na Faransawa suna goyon bayan wannan matakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu