Isa ga babban shafi
Faransa

Fabius ya karyata zargin yana da asusun ajiya a waje

Ministan Harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya musanta zargin da wata jarida ta yi cewar, yana da susun ajiya a wani banki da ke kasar Switzerland, a dai dai lokacin da Gwamnatin kasar ke bin fallasar da ya sa Ministan kasafin kudi, Jerome Cahuzac ya sauka daga mukamin sa.

Laurent Fabius kusa da  Jerôme Cahuzac wanda ya amsa yana da asusu ajiya a switzerland
Laurent Fabius kusa da Jerôme Cahuzac wanda ya amsa yana da asusu ajiya a switzerland Reuters/ RFI
Talla

Wata sanarwar da ministan ya rabawa manema labarai, ta nuna y yi watsi da zargin, inda ya ke cewa babu gaskiya ko kadan a ciki.

Kasar Faransa tace ta nemo hanyar kara tsaurara matakan kaucewa biyan haraji da wasu attajirai ke yi, sakamakon abin kunyar da aka samu, wanda ya girgiza gwamnatin shugaba Francois Hollande.

Ministan kudin kasar, Pierre Moscovici, yace Faransa za ta nemi ganin an kara musayar bayanai tsakanin bankunan kasashen Turai, don magance matakan da masu kin biyan haraji ke dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.