Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
An kaddamar da shirin farfado da salon kidan Duma a Nijar
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin kidan Duma, guda cikin al'adun jihar Maradi da ke kokarin gushewa.31/08/202310:12 -
An gudanar da bikin doya na shekara-shekara a Jamhuriyar Benin
Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon zai duba yadda aka gudanar ad bikin doya na shekara-shekara a Jamhuriyar Benin. Ana gudanar da wannan biki na doya a duk shekara musaman a ranar 15 ga watan Agusta a garin Savalou dake Jamhuriyar Benin. Tun asali dai daya daga cikin kabilun yankin da aka sani da kabilar Salman ne ke shirya wannan bikin na gargajiya domin nuna godiya da samun damuna mai albarka.22/08/202309:49 -
Dangantakar arewacin Najeriya da wasu kabilun kudancin kasar
Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan maako ya kawo batutuwa da dama da suka hada da irin dangantakar da ke tsakanin kabilun arewacin Najeriya da na kudancin kasar. Mazauna arewacin Najeriya da akasarinsu yan kasuwa ne,na gudanar da harakokinsu na kai da kawo daga wani yankin zuwa wanin yankin daban,to sai dai wasusu a maimakon fatauci,ba sun rungumi almajiranci da iya sani da suke da shi da nufin korewa bakin kuda ta hanyar zuwa kudancin kasar a wancan lokaci.15/08/202309:50 -
Alakar Barebari da turare wadda ta zama tamkar al'ada
Kamar dai yada muka saba a cikin Shirin za mu dubo halakar da ke tsakanin babar-bare da batun da ya shafi amfani da turare. Bayan haka shirin ya duba yadda auren kabilar Tubawa yake a al'adance.01/08/202309:49 -
Tarihin zuwan hausawan jamhuriyar Benin daga Najeriya
Shirin al'adu na wannan mako ya mayar da hankali kan yadda mahukuntan jamhuriyar Benin ke kokarin inganta al'adun su, da kuma habbaka bangaren yawon bude idanu.11/07/202310:01 -
Mahautan Nijer sun yi fice wajen iya gasa nama a Senegal
Sanin kowa ne dai, ko wace kasa ta duniya da irin sana'ar da mutanenta suka fi yin fice a cikinta fiye da sauran takwarorinsu na duniya. Mahautan kasar Jamhuriyar Nijer mazauna kasar Senegal na taka muhimmiyar rawa wajen iya gudaanar da Sana'ar gasa nama a kasar Senegal, dayan daga cikin manyan kasashe dake yankin yammacin nahiyar Afrika.A kan haka ne wakilinmu Salisu Isa da ya ziyarci kasar ya hada mana shiri kan yadda ake yaba sana'ar naman da yan kasar ta jamhuriyar Niger ke gudanarwa .05/07/202310:11 -
Yadda babban taron masarautar Hausawar Afrika ya gudana a Kano
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da bikin masarautar Hausawar Afrika a jahar Kano da ke tarayyar Najeriya, kuma a lokacin taron an gudanar da nade-nade da bama da akayi da zummar hada kan al'ummar Hausawa da ke kasashe daban daban.27/06/202310:15 -
Tasirin fasahar AI wajen samar da sauyi ga al'adun gargajiya
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali game da tasirin da sabuwar fasahar AI ta sanya na'urori basirar dan adam za ta yi ga tsarin al'adun gargajiya.16/06/202310:24 -
Al'adun Auren kabilar Bugaje a Jamhuriyyar Nijar
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adar auren Bugaje a Jamhuriyyar Nijar guda cikin al'adun da ke mutunta bukukuwan gargajiya da kuma dokokin hada zuriya.06/06/202310:06 -
Al'adu da sarautun gargajiyar Hausawa a garin Kumasi na kasar Ghana
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali ne kan al'adun al'ummar yankin Kumasi da ke kasar Ghana, yankin da ke kunshe da tarin al'ummar Hausawa a kasar ta yammacin Afrika.30/05/202309:37 -
Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan makon ya tattauna ne da kungiyar Gwape a jihar Neja
Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan makon ya tattauna ne da kungiyar Gwape a jihar Neja dake arewa maso tsakkiyar Najeriya, kungiyar da ke raya al'adun gargajiya na mutan wannan yanki.26/05/202309:55 -
Kananun Kabilu na hadewa da juna don kaucewa barazanar gushewa
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba ne kan yadda kananan kabilu ke dunkulewa a sassan Najeriya a wani yunkuri na habaka al'adunsu, wannan mataki na zuwa a dai dai lokacin da kananun kabilun ke fuskantar mamaya daga manya.16/05/202309:56 -
Mabanbantan abincin gado a kasashen Afrika
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yi nazari kan mabanbantan nau'ukan abinci da ake ci a wasu kasashen Afrika ta yamma kamar Ghana, Najeriya da Nijar.09/05/202309:56 -
Gasar musayar al'adu da harsuna tsakanin masoya tashar Radiyo Faransa
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya mayar da hankali kan gasar da masoya tashar radiyon Faransa RFI da aka fi sani da ''Club RFI'' suka shirya a birnin Lagos na Najeriya, wadda ke da nufin musayar al'adu da yaruka tsakanin mabanbantan masu sauraron tashar.04/04/202309:49 -
Ala'adar taimaka wa juna a tsakanin Hausawa da sauran kabilu a Togo lokacin Ramadan
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya mayar da hankali ne a kan tanade-tanaden al'adun Bahaushe, wadanda akasarinsu suka rungumi addinin Musulunci a game da tamakekeniya a lokacin azumin watan Ramadan. Shirin ya leka kasar Togo, inda ya tattauna da Hausa da ke zaune a wannan kasa tare da wasu kabbilu a game da hakan.28/03/202310:19
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.