Isa ga babban shafi

Nijar ta yi wa dubban yara rigakafin cutar Diptheria

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta rawaito cewa, hukumomin Nijar su shafe tsawon kwanaki hudu suna  gudanar da aikin rigakafin kamuwa da cutar sarkewar numfashi ta Diptheria a jihar Zinder da ke zama cibiyar annobar cikin shekaru 20 a kasar.

Rigakafin cutar sarkewar numfashi ta Diptheria.
Rigakafin cutar sarkewar numfashi ta Diptheria. picture alliance via Getty Image - picture alliance
Talla

Tun lokacin da cutar ta mashako ta fara barkewa a cikin watan Yuli a Nijar, ta kashe fiye da mutane 200 daga cikin mutane dubu 2 da 936 da suka harbu da ita  kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.

WHO ta ce, a ranar 20 ga watan Nuwamban nan ne, hukumomin kiwon lafiyar Nijar suka kaddamar da aikin rigakafin a Matameye da ke  Zinder wadda ke da kashi 48.7 na masu dauke da cutar ta Diptheria a kasar.

Ya zuwa ranar 24 ga wannan wata na Nuwamba, kimanin kananan yara dubu 300 ne daga matakin jarirai zuwa ‘yan shekara 14, aka yi wa rigakafin kamuwa da cutar, kuma adadin jami’an kiwon lafiyar da suka gudanar da wannan aikin ya kai dubu 1.

Wannan cuta ta Diptheria dai, na da matukar hadari kuma tana yaduwa ne cikin sauri, inda take haddasa zafin kirji da bushewar makoshi, baya ga zazzabi da kuma kumburin wuya da ciwon kai da yoyon hanci har ma da tari.

Sai dai rigakafin na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke shan radadin takunkuman da aka kakaba mata sakamakon juyin mulkin soji na ranar 26 ga watan Yuli, abin da ya haddasa karancin shigowar wasu kayayyaki da suka hada da magunguna ciki kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.