Isa ga babban shafi

Gidan rediyon RFI ya bude sabuwar tashar FM a yankin Tillaberi

Gidan Rediyon RFI ya fadada watsa shirye shiryensa da yake gabatarwa kai tsaye zuwa yankin Tillaberi da ke yammacin Jamhuriyar Nijar.

Na'urar Magana a dakin Labarai ta gidan Rediyon Faransa
Na'urar Magana a dakin Labarai ta gidan Rediyon Faransa RFI
Talla

Ci gaban da aka samu ya biyo bayan bude tashar FM akan mita 93.1, da gidan Rediyon na RFI yayi a yankin na Tillaberi.

Sabuwar tashar FM din dai ita ce ta 7 da RFI ya bude a Jamhuriyar Nijar, bayan wadanda suka shafe shekaru suna aiki a Yamai, Maradi, Zinder, Tahoua, Diffa da kuma Agadez.

Al’ummar yankin Tillaberi da Tera da yawansu ya kai mutane akalla miliyan 1.2 ne ake sa ran za su rika sauraron shirye-shiryen da tashar FM din za ta rika gabatarwa a cikin harsunan Faransanci, Hausa da kuma Fulatanci.

Yada shirye-shirye cikin harsunan kasashen Afirka, na daga  cikin hanyoyin da gidan Rediyon RFI ke amfani da su wajen isa ga masu sauraron da bas a daga cikin kasashe masu Magana da harshen Faransanci, ko kuma wadanda basu kware a yaren ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.