Isa ga babban shafi

RFI ta kaddamar da sabuwar manhajar 'RFI Pure Radio'

RFI ta kaddamar da sabuwar manhajarta ta 'RFI Pure Radio' wadda kacokan aka tanadar da ita  domin sauraren labarai da shirye-shirye kai-tsaye kuma za a iya samun ta daga yau a rumbunan manhajoji na 'App Store' da 'Google Play'.Tana dauke da sabon tsari  da sauye-sauye da saukin fahimta, ganin yadda aka tsara ta daidai da bukatuwar mutane ta sauraren sautuka ko da a halin zirga-zirga.

Za a iya samun manhajar a rumbunan App Store da Google Play.
Za a iya samun manhajar a rumbunan App Store da Google Play. © RFI
Talla

Wannan mahajar wadda baki dayanta kyauta ce, an tsara ta ne a matsayin dandalin saurare da ke bai wa mutane damar samun daukacin labaran RFI a cikin harshen Faransanci da sauraren harsuna 15.

Yanzu haka 'RFI Pure Radio' na dauke da shafin farko mai kunshe da bayanai kan daukacin sabbin kanun shirye-shirye cikin sautuka kuma tana nuna sabbin shirye-shirye da labarai da aka watsa na wannan rana, ga kuma damar samun muhimman shirye-shiryen sautuka na ainihi.

Sannan tana dauke da bangaren da za a samu rahotanni da babi-babi da shirye-shirye domin fahimtar labarai cikin sauki.

Kazalika wannan sabuwar manhajar tana bayar da damar sauke shirye-shiryen da za a iya sauraren su daga bisani ba tare a intanet ba, sannan za a iya laluben maudu’in da mai saurare ke bukata, yayin da za a iya gudanar da binciken cikin sauki.

Har ila yau, manhajar na bayar da damar lalubo takamammen shiri na kowanne lokaci, sannan za ta nuna muku bakin da gidan rediyon ya yi hira da su.

An tsara ta ne domin ta yi daidai da kowanne irin nau'in na’ura a duniya. Ma’aikatan France Medias Monde ne suka yi nazarin kirkiro wannan sabuwar manhajar domin ta biya bukatun dimbi mutane.

Tana bayar da damar sauraren shirye-shirye cikin nishadi tare da debe wa mai saurare kewa, har ta yi masa rakiyar kwarewa wajen sarrafa ta. Babban dalilin samar da manhajar shi ne karfafa sabon tsarin nan na shirye-shiryen sautuka a yanar gizo a sassan duniya musamman a nahiyar Afrika.

Wannan manhajar sautin, 100 bisa 100 ta cika duk wani muradi da manhajar RFI ke bukata da ya hada da daukacin shirye-shiryen rediyo a yanar gizo kamar (sauti, rubutu da bidiyo).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.