Boko Haram ta kashe masu hakar man fetir a Nijar
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, sun kashe ma’aikatan kamfanin Foraco 7 da ke aikin hakar rijiyoyin mai a garin Tumour da ke jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar.
Wallafawa ranar:
Harin wanda aka kaddamar a safiyar ranar Alhamis ya auku ne a dai dai lokacin da jami’an tsaron da ke kare lafiyar ma’aikatan kamfanin suka janye daga fadar magajin garin Tumour, wato masaukin ma’aikantan kamfanin na Foraco.
Maharan sun yi awon gaba da motocin kamfanin guda biyu , yayin da suka kama hanyar zuwa kan iyakar Nijar da Najeriya.
Garin Tumour ya kasance wani sansanin ‘yan gudun hijira tun bayan da ‘yan Kungiyar Boko Haram suka fara kai hare-hare a kasashen da ke yankin tafkin Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu