Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta bai wa Amurka damar girke jirage masu sarrafa kansu

Gwamnatin Nijar ta bukaci kasar Amurka ta girke jiragenta na sama masu sarrafa kansu a cikin kasar, da ke dauke da makamai, domin yaki da ’yan ta’adda a kan iyakar Mali.

Daya daga cikin jiragen yakin Amurka masu sarrafa kansu kirar MQ-9, yayinda yake shirin tashi zuwa kai hari a sassan kasar Afghanistan.
Daya daga cikin jiragen yakin Amurka masu sarrafa kansu kirar MQ-9, yayinda yake shirin tashi zuwa kai hari a sassan kasar Afghanistan. REUTERS/Josh Smith
Talla

Ministan tsaron kasar Kalla Mountari ne ya sanar da cewa ya shaidawa Amurka amincewar gwamnati akn fara amfani da jiragen wajen kai hare-hare.

Mountari yace wata tawagar sojin Amurka 12 da na Nijar 30 sun kai hari kan iyakar Mali inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama kafin kwanton baunar da aka yi musu.

Ministan yace sojojin na Amurka ba wai suna musayar bayanai ne da takwarorin su na Nijar kawai ba, suma suna shiga yakin idan hali yayi.

Cibiyar da jiragen Amurkan marasa matuki zasu rika tashi, zata kasance ne garin Agadez, inda a baya jiragen masu sarrafa kansu da ke shawagin leken asiri ne kawai ke tashi.

Kai hare-hare ta hanyar amfani da jirage masu sarrafa kansu na fuskantar suka a sassan duniya, saboda yadda a lokuta da dama ake samun kuskuren hallaka fararen.

Matakin dai ya sa wasu ‘yan kasar ta Nijar gudanar da zanga-zangar adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare a cikin kasarsu, da kuma matakin da gwamnati ta dauka bada damar fara kai wa ‘yan ta’adda farmaki da jiragen marasa matuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.