Isa ga babban shafi
Nijar

"Ya kamata Nijar ta yi koyi da Najeriya wajen yakar rashawa"

Ana cigaba da tafka muhawara kan batun yaki da cin hanci da rashawa a Jamhuriyar Nijar, domin kuwa yayinda wasu ke yabawa gwamnatin kasar kan shirinta, wasu na na da ra’ayin cewa batun yaki da cin hanci da kuma masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa na ci gaba da yin tafiyar hawainiya sakamakon yadda hukumomi suka nuna gazawa a wannan fage.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mahammadou Issoufou a birnin Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mahammadou Issoufou a birnin Abuja tamtaminfo.com
Talla

Hakan ta sanya wasu ke bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata shugaban kasar Issoufou Mahamadou ya yi koyi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, dangane da salon yaki da rashawar ko kuma yi wa tattalin arzikin kasa zagonsa.

Abdullahi Isaka shugaban wata Kungiyar ‘yan jaridu da ke yaki da cin-hanci ko rashawa a kasar ta Nijar ya yi y ace kamata yayi tun da jimawa wamnatin Nijar ta fara koyi Najeriya.

Isaka ya koka bisa cewar zuwa yanzu za’a iya cewa gwamnatin Nijar ta gaza wajen cika alkawarin da ta dauka na kawo karshen matsalar ta cin hanci da Rashawa, wanda a maimakon haka ma matsalar karuwa ta yi.

01:03

Abdullahi Isaka

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.