Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan gudun hijira da ke sansanin Tazalit na cikin zulumi

A Jamhuriyar Nijar, yan gudun hijara dake zaune a sansanin Tazallit mai nisan kilometa 400 da babban birnin kasar Yamai na cikin halin zulumi.  

"yan gudun hijira da ke sansanin Tazalit a Jamhuriyar Nijar
"yan gudun hijira da ke sansanin Tazalit a Jamhuriyar Nijar
Talla

Rahotani daga sansani na nuni cewa sojojin Nijar sun canza salon aiki, kuma ga dukkan alamu hakan ya haifar da fargaba tsakanin a ‘yan gudun hijrar.

Komawa kasar Mali ko cigaba da kasancewa a wannan sansani na Tazalit, tambayoyi ne da akasarin ‘yan gudun hijira dake a wannan wuri ke kokarin samun amsa a kai.

Yanayi da yan gudun hijrar suka samun kansu ya biyo bayan kazamin harin da ‘yan ta’adda suka kai kan ayarin dakarun Nijar ranar 7 ga watan Oktoba, harin da yayi sanadiyar mutuwar sojojin Nijar 22.
A wata sabuwa, wata majiya ta ce alamu dama sheidu bayan wani bicinken gaggawa sun nuna yadda wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da ba a tantance ba, ke taimakawa ‘yan ta’ada da bayanai.

Gwamnatin Nijar ta bakin Ministan cikin gida Bazoum Mohamed da ya kai ziyara yankin Tazalit dake tattare da ‘yan gudun hijira kusan 3,900 ya bayyana cewa sojojin Nijar za su sake dabaru, wanda zai taimaka wajen dakile wani sabon hari, ko kutse daga ‘yan ta’adda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.