Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar : An yi sakaci da harin Tazalit

Ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya ce an samu sakaci ta fannin bayanai da kuma bangaren jam’ian tsaro wanda ya ba ‘yan ta’adda samun nasara a harin da suka kai a garin Tazalit tare da kashe jami’an tsaron kasar 22 a kwanakin da suka gabata.

Ministan Cikin gidan Nijar Mohamed Bazoum a lokacin da ya kai ziyara a Bosso yankin da ke fama da hare haren Boko Haram
Ministan Cikin gidan Nijar Mohamed Bazoum a lokacin da ya kai ziyara a Bosso yankin da ke fama da hare haren Boko Haram ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Minista Bazoum wanda ke magana a lokacin da ya ziyarci karamin sansanin soji da ke Tazalit a cikin jihar Tawa arewacin kasar, ya ce lura da irin dubarun da aka yi amfani da su wajen kai harin, akwai alamun da ke tabbatar da cewa maharan suna da cikakkiyar masaniya a game da jami’an da ke samar da tsaro a sansanin da ke kunshe da ‘yan gudun hijirar kasar Mali.

Bazoum ya ce maharan sun fahimci salon aiki na jami’an tsaron sannan kuma sun sane da sansanin na ‘yan gudun hijira da ma sauran jama’ar da suke zaune a yankin.

Ya kara da cewa an samu sakaci a kowane mataki, daga jami’an tsaro da kuma sauran jama’a, duk da cewa yau shekaru uku ke nan da kafa sansanin a Tawa.

A ranar 7 ga watan Oktoba, wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai kusan 40, suka kai hari a sansanin da ke kusa da iyakar Nijar da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.