Nijar za ta kafa gwamnatin hadin kai
Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya ce a shirye ya ke domin kafa gwamnatin hadin-kan kasa bayan nasarar da ya yi a zaben da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Issoufou Mahamadou ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, yana fatan kafa gwamnatin da za ta kunshi ‘yan adawa domin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta, da suka hada da tsaro da kuma tattalin arziki.
To sai dai Salah Amadou na gungun ‘ya adawa, ya ce ba wani zabe da aka gudanar ballantana su amince da Issoufou a matsayin shugaba.
Ga abinda ya ke cewa
Muryar Salah Amadou na 'yan adawar Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu