Jakadan Najeriya a Morocco ya rasu
Jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli ya rasu yana da shekaru 42 a duniya, bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya da ya yi.
Wallafawa ranar:
Kafin rasuwar Alhaji Bamalli, shi ne Magajin Garin masarautar Zazzau na yanzu, kuma kane ga sarkin Zazzau da ke jihar Kaduna a Najeriya Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.
Wata sanarwa daga fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau ta ce Mansur Nuhu Bamalli ya mutu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin Lagos, a yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Morocco.
Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da lokacin jana’izarsa a nan gaba kadan.
Bamalli, wanda tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya nada shi a watan Oktoban shekarar da ta gabata ya rasu ya bar mata guda da ‘yaya biyu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu