Shugaba Tinubu ya janye daukacin jakadun Najeriya dake kasashen duniya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya janye daukacin jakadun kasar dake kasashe daban-daban.Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana matakin ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Alkasim Abdulkadir, a wannan Asabar.
Wallafawa ranar:
A watan Yulin shekarar 2020 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada jakadu 83 wadanda suka kunshi ma’aikatan diflomasiya 41 da jakadun siyasa 42 zuwa kasashe daban-daban.
An tura jami’an diflomasiyyar ne bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da su kamar yadda sashi na 171(2) (1c) da karamin sashe na 4 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Sanarwar da ta tabbatar da kiranye ga ilahirin jakadun ta ce: hakan na da nasaba da wasikar janye jakadan Najeriya a Burtaniya, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya yi karin haske kan cewa duk jakadun su dawo gida bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wasikar mai dauke da ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2023, Ministan Harkokin Waje ya sanar da kawo karshen aikin Ishola a kasar Ingila kamar yadda shugaban kasar ya bukaci ya yi..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu