Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya aika wa majalisa sunayen jakadunsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar dattijan kasar da sunayen mutane 46 don tantance su a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari statehouse
Talla

Shuagaban majalisar Sanata, Bukola Saraki da ke karanta wasikar a zauren majalisar ya ce, wasu daga cikin mutanen da Buhari ya aiko, sun hada da Pauline Tallen da Olorunibe Namora da Usman Bugaje da Yusuf Tugar da Musa Ibeto.

Wadannan mutanen dai na daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar yakin neman zaben shugaba Buhari.

Ga dai cikakken jerin sunayen mutanen da ake bukata su wakilici kasar a kasashen ketare.

1. Nurudeen Mohammed daga jihar Kwara
2. Jamila Ahmadu-Suka daga jihar Sokkoto
3. Suleiman Hassan daga jihar Gombe

4. Yusuf Tugar daga jihar Bauchi
5. Usman Bugaje‎ daga jihar Katsina
6. Uzoma Emenike daga jihar Abia
7. Clifford Zirra daga jihar Adamawa
8. Godwin Umo daga jihar Akwa Ibom
9. Christopher Okeke daga jihar Anambra
10. Baba Madugu daga jihar Bauchi
11. Stanley Diriyai daga jihar Bayelsa
12. Enyantu Ifenne daga jihar Benue
13. Mohammed Hayatuddeen daga jihar Borno
14. Etuborn Asuquo daga jihar Cross River
15. Francis Efeduma daga jihar Delta
16. Jonah Odo daga jihar Ebonyi
17. Uyagwe. Igbe daga jihar Edo
18. Ayodele Ayodeji daga jihar Ekiti
19. Chris Eze daga jihar Enugu
20. Muhammad Dalhatu daga jihar Jigawa
21. Mohammad Yaro daga jihar Kaduna
22. Deborah Iliya daga jihar Kaduna
23. Farfesa D. Abdulkadir daga jihar Kano
24. Haruna Ungogo daga jihar Kano
25. Isa Dodo daga jihar Katsina
26. Tijani Bande daga jihar Kebbi
27. Y.O Aliu daga jihar Kogi
28. Mohammed Yisa daga jihar Kwara
29. Modupe Irele daga jihar Lagos
30. Musa Mohammad daga jihar Nasarawa
31. Ade Asekun daga jihar Ogun
32. Sola Iki daga jihar Ondo
33. Adegboyega Ogunwusi daga jihar Osun.
34. Ashimiyu Olaniyi daga jihar Oyo
35. Haruna Bawa Abdullahi daga jihar Plateau
36. Orji Ngofa daga jihar Rivers
37. Sylvanus Adiewere Nsofor daga jihar Rivers
38. Kabiru Umar daga jihar Sokkoto
39. Mustapha Jaji daga jihar Taraba
40. Zanna Bura daga jihar Yobe
41. Garba Gajam daga jihar Zamfara
42. Abdullahi Garbasi daga jihar Zamfara
43. Pauline Tallen daga jihar Plateau
44. Olorunibe Mamora daga jihar Lagos
45. Musa Ibeto daga jihar Niger
46. George Oguntade daga jihar Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.