Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan majalisar Najeriya sun goyi bayan A'isha Buhari

Wasu mambobin majalisar wakilan Najeriya sun goyi bayan uwargidan shugaban kasar, A’isha Buhari kan sukar da ta yi wa gwamnatin mai gidanta.

Uwargidan shugaban Najeriya, A'isha Buhari da mijinta shugaba Muhammadu Buhari
Uwargidan shugaban Najeriya, A'isha Buhari da mijinta shugaba Muhammadu Buhari greenwhitegreennews.com
Talla

Mambobin majalisar sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi aiki da shawarar da A’isha ta ba shi don gyara tsarin tafiyar da mulkin kasar.

Shugaban kwamitin kula da kasafin kudin daukar dawainiyar majalisar, Timotty Golu ya bayyana cewa, A’isha ta fi kowa kusanci da mijinta, abin da ya ba ta damar fahimtar sa yadda ya kamata.

Mr. Golu ya kara da cewa, matar shugaban ta fada masa gaskiyar da mutanen da ke kewaye da shi ba su fada masa ba kuma ta dauki matakin ne saboda kaunar da ta take yi wa Buhari a matsayinta na matarsa.

A hirar da ta yi da kafar yada labarai ta BCC, Mrs. Buhari ta bayyana cewa, akasarin mutanen da shugaban ya nada kan mukaman siyasa bai san su ba kamar yadda ita ma ba ta san su.

Sannan ta ce, ba za ta goya masa baya ba a zaben shekarar 2019 matukar al'amuran ba su sauya ba.

Sai dai a martanin da ya mayar mata, shugaba Buhari ya bayyana matarsa a matsayin mai dafa masa abinci da kuma kula da cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.