Isa ga babban shafi

Katsina ta kaddamar da matasa 'yan sa-kai domin samar da tsaro

Gwamnatin Jihar Katsina dake Najeriya ta kaddamar da wasu matasa ‘yan sa-kai kusan 1,500 da ta horar domin gudanar da aikin tsaro a jihar dake fama da matsalar ‘yan ta’adda. 

Katsina na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Katsina na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro. © Bashir/RFI
Talla

Gwamnan Jihar Malam Dikko Rada ya kaddamar da matasan wadanda jami’an tsaron soji da ‘yan sanda suka horar lokacin wani gagarumin bikin da ya samu halartar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jihohi. 

Bayan horar da jami’an sakan, gwamnatin Katsina ta kuma saya musu motoci da babura da makamai domin ganin ta taimaka musu wajen sauke nauyin da ya rataya akan su na samar da tsaron da ake bukata. 

Kwamishinan yada labarai na jihar, Bala Zango, yace wadannan matasa da aka horar za suyi aiki tare ne da sojoji da ‘yan sanda wajen ganin sun tallafa musu domin shawo kan matsalar da ta addabi jihar. 

04:57

Muryar Bala Zango

Jihar Katsina na daga cikin jihohin dake yankin arewa maso yammacin Najeriya wadanda ke fama da matsalar ‘yan ta’adda wadanda suka hana zaman lafiya a wasu kananan hukumomin ta. 

Tsohuwar gwamnatin Aminu Bello Masari da ta gabata, ta kaiga yin sulhu da wasu daga cikin ‘yan ta’addan wadanda suka sanar da aje makaman su, amma kuma daga bisani suka sake komawa daji. 

Yayin gudanar da yakin neman zaben sa, gwamna Dikko Rada ya sha alwashi kashe duk abinda jihar ta mallaka wajen ganin an shawo kan wannan matsala ta tsaro wadda ta hana zaman lafiya da kuma gudanar da harkokin ci gaba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.