Isa ga babban shafi

Najeriya: Sojoji ba su da kwarewa wajen tattara shaidu kan 'yan ta'adda - Arase

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Sandan Najeriya Solomon Arase, ya ce sojoji da ake turawa yankuna da ‘yan ta’adda ke tada kayar baya musamman yankin Arewa maso Gabas, ba su da horo da sanin makamar tattara shaidu da hujjoji kan masu aikata laifi, lamarin da ya ce ke ta’azzara ayyukan ta’addanci.

Wannan hoto ne dake nuna mayakan kungiyoyi dake ikirarin jihadi, AFP bata iya tantance inda aka dauke shi ba ko lokaci.
Wannan hoto ne dake nuna mayakan kungiyoyi dake ikirarin jihadi, AFP bata iya tantance inda aka dauke shi ba ko lokaci. AFP - HO
Talla

 

Arase, wanda tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda ne, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake sakin ‘yan ta’adda su koma cikin al’umma ba tare da cikakken bayyanansu ba da sunansu sun tuba, yana mai cewa a karshe akasarinsu suna komawa ruwa, lamarin dake haifar da illa ga yankin.

Don haka yake ganin ya kamata ‘yan sanda su karbe ragamar ayyukan yaki da ta’addanci da sauran laifuffuka daga hannun sojoji, yana mai cewa ‘yan sanda na da horo na musamman kan wuraren da ake aikata laifuka, da tattara shaidu da gurfanar da masu aikata laifuka daban-daban da ya sha bamban da tsarin aikin sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.