Isa ga babban shafi

Akalla mutane miliyan 6 na neman agajin gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 6 ne ke bukatar taimakon gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya, tana mai kashedin cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba matsalar jinkai za ta ta’azzara  yankin da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi suka daidaita.

'Yan gudun Hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram
'Yan gudun Hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban hukumar jinkai ta majalisar, Matthias Schmale, a yayin jawabinsa ga wani taron manema labarai a Geneva ya ce dole ne a tashi tsaye kada yanayin da ake ciki a arewa maso gabashin Najeriya ya munana, yana mai cewa mutane kimanin miliyan 4 da dubu dari 3 na fuskantar  matsalar matsanacin yunwa a jihohin   Borno, Adamawa da Yobe.

Tun daga shekarar 2009 ne aka shiga mummunar bata kashi tsakanin sojin Najeriya da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka hada da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar.

An kiyasta cewa sama da mutane dubu 40 ne aka kashe a wannan rikici na ta’addanci ya zuwa yanzu, kuma mutane miliyan 2 suka daidaita, abin da ke nuni da daya daga cikin munanan matsalar jinkai a cikin karni na 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.