Isa ga babban shafi

Kwamandojin 'yan ta'adda sun mutu a fadan Boko Haram da ISWAP

Akalla mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP 41 ne suka mutu, cikin su har da kwamandojinsu sakamaakon wani fada da ya barke a tsakaninsu ranar Laraba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Majiyoyi sun ce  ‘yan ta’addar ISWAP, wadanda suka yi amfani da kwale-kwale da dama ne suka kai wa tsagin kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Bakoura Buduma hari a yankin Duguri na Karamar Hukumar Kukawa ta jihar Bornon.

Kukawa, wanda ke karkashin mazabar dan majalisar dattawa ta arewacin Borno, na da nisan kilomita 130  daga Maiduguri, babbaann birnin jihar.

Nagartattun majiyoyi sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda wani kwararre a kan abin da ya shafi  yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya ce dukkanin bangarorin da suka ba hammata iska sun yi asarar mayaka har da kwamandoji.

Makama ya ce ISWAP ta fi yi wa Boko Haram mummunar aika-aika, sabodaa ta kasha dimbim kwamandodinta.

Ya ce, kwamandojin da suka mutu sun hada da Modu Kayi da Abbah Musa da Isa Muhammed da Ibrahim Ali da Kanai Zakariya da Bula Salam da Isuhu Alhaji Umaru da Dogo Salman da Abdulrahman Malam Musa da dai  sauransu.

Rikici tsakanin kungiyar  Boko Haram da ISWAP ya zama ruwan dare a ‘yan kwanakin nan, musamman a  dajin Sambisa na jihar Borno da kuma yankin tafkin Chadi.

Yanzu  ISWAP ce  ke kara samun karfi tare da nasara, biyo bayan sauya sheka da wani kwamandanta mai muhimmanci, Abou Idris ya yi daga Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.