Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan ta'adda sun kashe mutane 13 a jihar Borno

Wasu mahara da ake zargi mayaka masu ikirarin jihadi ne sun kashe mutane 13 ciki har da sojoji 3 a  jihar Borno  da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda mayakan sa kai da ke aiki da sojojin Najeriya suka  bayyana a Lahadin nan.

Wasu dakarun sojin Najeriya akan hanyar Konduga zuwa Bama a jihar Borno. 31/8/2016.
Wasu dakarun sojin Najeriya akan hanyar Konduga zuwa Bama a jihar Borno. 31/8/2016. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kai wannan harin ne a cikin talaitainin daren  Asabar zuwa wayewar garin Lahadi a kan wani sansani da ke Wulari, wani kauye da ke kusa da garin Konduga na jihar Borno.

Daya daga ciki jagororin ‘yan sa kai, Ibrahim Liman ya ce ‘yan ta’addan sun yi amfani da duhun dare da kuma na masara da ke gonakin da ake daf da yin girbi ne wajen kai wa sansanin farmaki.

Liman ya ce dakarun Najeriya sun tinkare ‘yan ta’addan, inda  aka yi mummunan ba-ta-kashi, lamarin da ya yi sandin mutuwar sojoji 3.

Wasu majiyoyi sun ce ko a yammacin Asabar, sai da ‘yan ta’adda suka yi wa wasu manoma kawanya a yayin da suke aiki a wata  gona, inda  suka kashe mutane 10 da ke aiki  a cikin gonar.

Kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun tsananta hare-hare a kan masu saran itace, manoma, masunta da ‘yan gwangwan, suna mai zarginsu da yi musu leken asiri.

Akalla mutane dubu 40 ne suka mutu sakamakon rikicin ‘yan ta’adda da aka shafe shekaru 14 ana yi  a Najeriya, rikicin da ya bazu zuwa makwaftanta Nijar, Kamaru da Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.