Isa ga babban shafi
Najeriya-Tsaro

Sojin saman Najeriya sun kashe wasu jagororin 'yan ta'adda

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta halaka wasu jagororin kungiyar ‘yan ta’adda na ISWAP a wasu hare haren da ta kai garuruwan Jubillaram da Alinwa a arewacin jihar Borno.

Jirgin sintiri na  ATR 42-500 na sojin saman Najeriya
Jirgin sintiri na ATR 42-500 na sojin saman Najeriya AFP Photo/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar dakarun Operation Lafiya Dole a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin kasar ta kashe ‘yan bindiga 13 tare da kame 8.

Wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ta ce rundunar ta samu kashe jagororin na ISWAP din ne yayin wani taron da suke gudanarwa biyo bayan wasu bayanan sirri da ta samu.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen shugabannin ‘yan ta’addan da aka kashe ba, ko kuma takamammen matsayinsu a kungiyar ISWAP, amma ta ce an kai samamen ne bayan ingatattun bayanai na sirri da soji ta samu na cewa shugabannin mujahidan na gudanar da taruka dabam dabam har biyu a Jubillaram da Alinwa a karamar hukumar Marte a jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.