Isa ga babban shafi
Najeriya

Jirgin sojin saman Najeriya ya kashe 'yan Boko Haram

Jirgin sama mara matuki na rundunar sojin sama Najeriya ya yi lugudan wuta kan kungiyar Boko Haram a jiya talata a kusa da dajin Sambisa da ke arewa maso gabashin kasar, inda ya kashe mayakan kungiyar da dama tare da lalata makamansu.

Jirgin sojin sama na Najeriya
Jirgin sojin sama na Najeriya naij.com
Talla

Direktan yada labarai na sojin saman kasar, Ayodele Famuyiwa ya bayyana haka a cikin wata sanawar da ya fitar.

Sanawar ta ce, jirgin ya kaddamar da farmakin ne kan kungiyar a dai dai lokacin da ya ke gudanar da aikin tattara bayanan sirri, yayin da ya hangi taron mayakan Boko Haram a yankin Garin Moloma mai tazarar kilo mita guda daga dajin Sambisa.

Rundunar sojin ta bayyana wannan farmakin a matsayin gagarumar nasara a yakin da ake yi na kokarin kakkabe kungiyar Boko Haram a Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

A bangare guda, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile hare haren kunar bakin wake bayan sun kama wasu mutane da ke kokarin shiga birnin Maiduguri na jihar Borno dauke da bama bamai a jikinsu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.