Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba yadda zaa yi nasara akan Boko Haram da makaman jabu

Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin tsohon shugaba Goodluck Jonathan na cewa makaman da gwamnatinsa ta siya ne ake anfani dasu wajen yakar kungiyar Boko Haram a yanzu

Wani wuri da aka gano da tarin makaman Boko Haram a dajin Sambisa
Wani wuri da aka gano da tarin makaman Boko Haram a dajin Sambisa AFP/Armée nigériane
Talla

A cewar Ministan yada labaran kasar Lai Mohammad, asali ma makaman na jabu ne kuma babu yadda za’a iya anfani dasu har a sami irin nasarar da aka samu yanzu haka akan mayakan na Boko Haram.

Lai ya sanar da hakan ne a yayin da ya ke ziyara aiki a garin Abeokuta dake jahar Ogun dake kudu maso yammancin kasar.

Rahotanni a kasar sun nuna yadda rashin ingantatun makamai suka taka rawa a asarar rayukan al'umma dama dukiya a tsawon shekaru da kungiyar Boko Haram ta dauka tana kai munanan hare-hare musanman a yankin arewa maso yammancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.