Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun rikita 'yan ta'adda

Dakarun sojin Najeriya sun yi wa mayakan Boko Haram da na IS mummunar barna a arewa maso gabashin Najeriya.

'yan Boko Haram da suka tuba a Najeriya.
'yan Boko Haram da suka tuba a Najeriya. Daily Post
Talla

Wata sanarwa daga kakakin runduna ta musamman da ke yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Kanar Aminu Iliyasu ta ce dakarun na Najeriya sun yi gagarumar nasara a yakin da suke da ayyukan ta’addanci.

Kanar Iliyasu ya ce sojin Najeriya sun jaddada nasarar da suka samu kan ‘yan ta’adda sakamakon kara azama da suka yi a garuruwan Damboa, Garkida a jihohin Borno da Adamawa.

Ya ce rike wuta da suka yi wa ‘yan ta’addan ya ruda su har sai da sabani ya shiga tsakaninsu a bangare daya, da kuma tsakaninsu da takwarorinsu ‘yan ta’adda a daya bangaren.

Iliyasu ya bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar Boko Haram biyu sun mika wuya sakamakon wannan aiki da sojin Najeriya suka yi, kuma wadanda suka mika wuyan sune: Musa Mohammed mai shekaru 21 da Maina Liman mai shekaru 35, kuma sun mika wuya ne ga dakarun bataliya ta 202 a Tashar Goto a karamar hukumjar Bama ta jihar Borno a ranar 5 ga watan Maris.

Ya ce ‘yan ta’addan da suka mika wuya sun ce su yaran Nakib ne, wani kwamandan Boko Haram a kauyen Bula Umar. Ya kara da cewa, ‘yan ta’addan sun shaida wa masu bincike cewa da dama ‘yan uwansu na gararamba cikin daji saboda sun gaji da al’amarin ta’addanci, kuma suna neman yin saranda, yayin da da dama daga cikinsu sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.