Isa ga babban shafi

'Yan Hisba sun kame matasan da suka shirya auren jinsi a Kano

‘Yan Hisbah a jihar Kano da ke tarayyar Najeriya sun sanar da kame wasu matasa 19 a yayin da suke tsaka da shirya auren jinsi.

Taswirar masararutar Kano.
Taswirar masararutar Kano. © Kano Emirate council
Talla

Kakakin hukumar Hisbar ta jihar Kano, Lawan Ibrahim Fagge ya ce daga cikin wadanda aka kama, kuma su ke tsare yanzu haka a hannunsu, akwai mata 15 da maza 4, wadanda ba su wuce shekaru 20 da wani abu ba kowanne, kuma an kama su ne a wata cibiyar shirya bukukuwa a birnin.

Ibrahim Fagge ya ce jami’an Hisba sun kai samame wajen shirya bikin ne a lokacin da ake tsaka da sha’ani, inda suka kame mutanen, ciki har da kirjin bikin, sai dai wadanda ake daf da daura auren nasu sun arce, ko da ya ke ya ce ana ci gaba da lalubensu.

Wadanda ake zargin da suka ce ‘yan rawa ne su, sun musanta zargin, su na mai cewa sun shirya ruguntsimin taya daya daga cikin abokansu murnar samun mukamin mataimakin shugaban wani gidan rawa ne.

Jihar Kano da ke arewa maso yammmacin Najeriya, na daya daga cikin jihohin da akasari mazaunansu Musulmai ne, inda ake aiki da dokokin shari’ar Musulunci, kuma  karkashin dokar addinin na Islama akan zartas da hukuncin kisa kan duk wanda aka samu da laifin auren jinsi duk da cewa har zuwa yanzu babu wanda aka zartaswa makamancin hukuncin.

‘Yan hisba a jihar Kano sun sha kama wadanda ake zargi da auren jinsi, sai dai har yanzu babu wanda aka gurfanar a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.