Isa ga babban shafi
Faransa - auren jinsi

Masu kare auren jinsi a Faransa na shirin maka Zemmour gaban kuliya

Kungiyar masu rajin kare auren jinsi a Faransa na shirin maka dan takarar shugabancin kasar mai tsattsauran ra’ayi Eric Zemmour kotu, saboda zargin sa da karyata cewa an yiwa masu auren jinsi kawanya lokacin da dakarun Nazi suka mamaye Faransa a yayin yakin duniya na biyu.

Dan takarar neman shugabancin Faransa Eric Zemmour yayin gangamin siyasa, 05/02/2022 a Lille.
Dan takarar neman shugabancin Faransa Eric Zemmour yayin gangamin siyasa, 05/02/2022 a Lille. AP - Michel Spingler
Talla

Kungiyoyin rajin kare hakkin masu auren jinsin 6 ne suka yi wannan barazana, suna masu cewa babban laifi ne karyata cewa an ci zarafin masu auren jinsin a zamanin yakin duniya na biyu, duk da cewa a hukumance Faransa bata dauki matsaya kan wannan batu ba.

A cikin wani tsokaci na Zemmour da aka wallafa, wanda cikin sa ne ya yi wadannan kalamai, dan takaran ya kuma amince da wani dan siyasa da ya bayyana ikirarin cewa a ci zarafin masu auren jinsi a matsayin al’amara.

Kungiyoyin sun kuma dage kan cewa Zemmour ya bijiro da wadannan kalamai ne don kawai ya sake jaddada tsattsauran ra’ayin da yake da shi.

Sai dai kuma tuni Lauyansa Olivier Pardo ya ce bai ma sami takaradar koken a hukumance ba, yana mai cewa wadannan kalamai, ba wai kai tsaye sun fito daga bakin wanda ya ke karewar ba, sai dai kawai ya amince ne da su, kuma yana da damar yin hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.