Isa ga babban shafi

Majalisar Wakilan Rasha ta haramta yada farfaganda kan auren jinsi

Majalisar wakilan Rasha a yau alhamis ta amince da sabuwar dokar da ta haramta duk wani yunkurin yada farfagandar da ke goyon bayan auren jinsi a sassan kasar.

Majalisar Wakilan Rasha.
Majalisar Wakilan Rasha. via REUTERS - RUSSIAN STATE DUMA
Talla

Sabuwar dokar wadda aka kadawa kuri’a ba tare da hamayya ba, Mosow ta tsaya kai da fata game matsayarta na haramta duk wata alakar auratayya da ta sabawa yadda dan adam y agada tsawon shekaru a ban kasa.

Da ya ke jawabi game da sabuwar dokar kakakin majalisar wakilan ta Rasha Vyacheslav Volodin ya ce akwai hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da laifin wanda ya saba da halittar dan adam.

Majalisar ta Rasha cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Telegram ta ce sabuwar dokar za ta kange al’ummar kasar musamman masu tasowa a nan gaba daga mummunar akidar wadda Amurka da kasashen Turai ke son karfafata a Duniya.

Dokar dai na bukatar goyon bayan Majalisar Dattijai da kuma sanya hannun shugaba Vladimir Putin gabanin fara aiki da ita tare da hukunta wadanda aka samu da wannan dabi’a ko kuma farfagandarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.