Isa ga babban shafi

Wani dan bindiga a Amurka ya kashe wasu masu auren jinsi 5 a gidan rawa

Wani dan bindiga a Amurka ya harbe mutane 5 har lahira bayan da ya kutsa kulob din masu auren jinsi a jihar Colorado, amma lamarin ya takaita bayan da wasu da ke cikin kulob din suka yi jarunta wajen dakile aika aikaarsa,  kamar yadda ‘yan sanda  suka shaida wa wani taron manema labarai ranar Lahadi.

Wani mamba a kungiyar LGBTQ masu auren jinsi guda.
Wani mamba a kungiyar LGBTQ masu auren jinsi guda. AFP
Talla

‘Yan sanda sun ce mutane 25 sun jikkata a harin da dan talikin ya kai jim kadan gabanin tsakiyar daren asabar, inda suka ce akwai adadin mutanen da ba a tantance ba, wadaanda suke cikin mawuyacin hali.

Shugaban ‘yan sandan Adrian Vasquez ya shaidawa taron manema labarai cewa wanda ake zargin ya shiga kulob din kuma nan take ya fara harbi.

Wanna harin shine na baya bayan nan a tarihin hare haren da ake kai wa taron ‘yan luwadi da madigo a Amurka, mafi muni a cikinsu shine wanda mutane 49 suka mutu a wani gidan rawa na Orlando a jihar Florida a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.