Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Masu dauke da cutar coronavirus sun yi zanga-zanga a Gombe

Wasu masu dauke da cutar coronavirus da aka killace a Jihar Gombe dake Najeriya yau sun gudanar da zanga zanga, inda suka fice daga inda aka aje su saboda abinda suka kira rashin kula mai kyau daga gwamnati.

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa. World Health Organization
Talla

Jaridar Daily Trust tace mutane kusan 20 dauke da sanduna sun fasa inda aka ajiye su a garin Kwadon dauke da sanduna, inda suka tare hanyar Gombe zuwa Biu suna zargin hukumomin lafiyar dake kula da su da kin basu magani.

Masu zanga zangar sun ce kafin gano cewar suna dauke da coronavirus, suna fama da wasu cututtuka da suke kula da su, amma sai aka yi watsi da su yau kusan mako guda kenan.

Jaridar Daily Trust tace ta ga ma’aikatar lafiyar dake kula da wadannan mutane ba tare da sanya kayan dake kare su daga kamuwa da wannan cuta ba, banda kyallen rufe baki da hanci.

Sai dai kwamishinan yada labaran Jihar Gombe Alhassan Ibrahim yace masu zanga-zangar basu fahimci irin cutar da suke dauke da ita bane, yayin da yayi watsi da zargin cewar ba’a kula da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.