Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Akwai alaka tsakanin mace-macen Kano da coronavirus - Dr Gwarzo

Tawagar kwararrun likitocin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da ita zuwa Kano domin yakar annobar coronavirus, tace akwai alaka mai karfi tsakanin mace-macen da aka rika samu a jihar da cutar.

Daya daga cikin makabartun dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
Daya daga cikin makabartun dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano. Daily Trust / Richard P. Ngbokai
Talla

Yanzu haka dai tawagar kwararrun dake Kanon suna cigaba da ayyukansu.

Yayin zantawa da wakilinmu Abubakar Isa Dandago a baya bayan nan Dr Sani Gwarzo, daya daga cikin tawagar kwararrun likitocin yace duk da cewa har yanzu suna kan bincike, sun soma samun kwararan hujjojin dake alakanta mace-macen da aka gani a jihar ta Kano da annobar coronavirus.

03:38

Dakta Sani Gwarzo kan alakar mace-macen Kano da coronavirus

Abubakar Issa Dandago

A karshen watan Afrilu, gwamnatin Najeriya ta sanar da soma bincike domin gano musabbabin mace-macen da aka yi fama da su a Kano, inda a cikin kwanaki biyu, aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 150 a jihar, matuwar da a waccan lokacin wasu suka danganta da cutar COVID-19.

Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacinda har yanzu wani bangare na mutane ciki har da al’ummar jihar ta Kano ke ganin batun annobar coronavirus zuki ta malle ce kawai ake musu, domin amfani da damar kila wajen wawure dukiyar al’umma, ko kuma kawai ana yin hakan ne domin takurasu.

Bayanai sun tabbatar da cewar rashin yadda ko gaskanta annobar ta coronavirus ya sanya har yanzu wasu mutane basu daina shiga cinkoson jama’a ba, musamman a wajen jana’iza da kuma Masallatai, duk da cewa kwararru kan lafiya suna nanata gargadin da a kiyaye aikata hakan zuwa wani lokaci a nan gaba.

A baya bayan nan ne mataimakin gwamnan Borno Umar Kadafur, ya koka kan yadda har yanzu, akwai wani bangare na al’ummar jihar da basu yadda cewar cutar COVID-19 ko coronavirus gaskiya bace, yanayin da ya kamanta da yadda a shekarun baya wasu daga cikin al’ummar jihar suka raina barazanar kungiyar Boko Haram, wadda daga bisani ta addabi yankin arewacin Najeriya, musamman arewan maso gabashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.