Isa ga babban shafi
Najeriya

Adadin masu coronavirus yayi karuwar bazata a Kano

A karon farko yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 204, adadi mafi yawa a rana guda.

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa. MAURIZIO DE ANGELIS/SCIENCE PHOTO LIBRARY
Talla

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya tace daga cikin sabbin mutanen 204 da suka kamu da cutar ta coronavirus a jiya alhamis, mutane 80 sun fito ne daga jihar Kano, yayinda Lagos ke da mutane 45, abinda ya kara adadin wadanda suka harbu a Najeriya gaba daya zuwa dubu 1 da 932, kuma 58 daga cikinsu sun mutu, yayinda 319 suka warke.

Daga cikin sabbin adadin na jiya akwai mutane 12 a Gombe, 9-9 a Bauchi da Sokoto, 7-7 a Edo da Borno, 6-6 a Rivers da Ogun, 4-4 a Abuja da Akwa ibom da Bayelsa, sai 3 a Kaduna, bibbiyu a Oyo da Delta da Nasarawa, yayinda Ondo da Kebbi ke da mutum guda-guda.

Wadannan alkalumma na nuna cewar Lagos ke sahun gaba a jimillar wadanda cutar coronavirus ta kama da mutane 976, sai Kano a matsayi na biyu da mutane 219, sai Abuja mai mutane 178, Gombe na da 76, Borno na da 66, Ogun na da 56, Edo na da 44, Katsina na da 40, Bauchi 38, Sokoto 36, Kaduna 35, yayinda Akwa Ibom 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.