Isa ga babban shafi
Coronavirus

Karin mutane 196 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da samun sabbin mutane 196 da suka kamu da cutar coronavirus jiya laraba a wasu sassan kasar.

Cibiyar kula da masu dauke da cutar coronavirus a jihar Legas dake Najeriya.
Cibiyar kula da masu dauke da cutar coronavirus a jihar Legas dake Najeriya. Pius Utomi Ekpei/AFP via Getty Images
Talla

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya tace daga cikin sabbin adadin 196 da aka samu, 87 na birnin Lagos ne, sai 24 a Kano, 18 a Gombe, 17 a Kaduna da kuma 16 a Abuja.

Sauran sun hada da 10 a Katsina, 8 a Sokoto, 7 a Edo, 6 a Barno, kana guda-guda a Jihohin Yobe da Ebonyi da kuma Adamawa, abinda ya kawo adadin mutanen da suka harbu da cutar a Najeriya zuwa dubu 1 da 728, daga cikinsu kuma 307 sun warke wadanda tuni sallame su, yayinda mutane 51 suka mutu.

Ya zuwa yanzu cutar ta ratsa daukacin Jihohin Najeriya banda Kogi da Cross Rivers, yayinda Lagos ke sahun gaba da mutane 931 da suka kamu, sai Abuja mai 174, sai Kano mai 139, da Gombe mai mutane 64, sai Barno mai mutane 59, sannan Katsina mai guda 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.