Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an kiwon lafiyar Najeriya 113 sun kamu da coronavirus

Gwamnatin Najeriya tace ma’aikatan lafiya 113 dake yaki da wannan annoba ta coronavirus sun kamu da cutar.

Wata jami'ar lafiya rike da kwalbar daya daga cikin magungunan da kwararru ke nazari akai don shawo kan annobar coronavirus.
Wata jami'ar lafiya rike da kwalbar daya daga cikin magungunan da kwararru ke nazari akai don shawo kan annobar coronavirus. Reuters
Talla

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana sabon adadin mai tayar da hankali, sakamakon karuwar da yayi daga jami’an lafiya 40 da a baya aka tabbatar sun kamu da cutar a makon jiya.

Ministan ya gargadi ma’aikatan kula da lafiya cewar, wadanda aka horar kan yadda za a kula da masu dauke da wannan cuta ta coronavirus kawai ke da hurumin duba wadanda suka kamu ita, inda ya kuma gargadi asibitoci masu zaman kansu akan yin gaban kansu wajen dawainiyar da masu cutar ta corona.

A ranar alhamis 30 ga watan afrilu, adadin wadanda suka harbu da coronavirus a Najeriya gaba daya ya karu zuwa dubu 1 da 932, kuma 58 daga cikinsu sun mutu, yayinda 319 suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.