Isa ga babban shafi

Adadin wadanda coronavirus ta kama a Najeriya ya kai dubu 1,337

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace an samu sabbin mutane 64 da suka kamu da cutar coronavirus a jihohin kasar 5.

Wani matashi sanye da kyallen rufe baki da hanci a birnin Abuja dake Najeriya. 20/3/2020.
Wani matashi sanye da kyallen rufe baki da hanci a birnin Abuja dake Najeriya. 20/3/2020. AFP - Kola Sulaimon
Talla

Sanarwar hukumar ta NCDC ta ce jihohin sun hada da Legas mai mutane 34 da suka kamu, sai Abuja mai 15, yayinda kuma mutane 11 suka kamu Barno. Sai kuma Taraba da Gombe masu mutane bibbiyu.

Karin mutane 64 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya sanya jimillar yawan wadanda annobar ta harba kaiwa dubu 1 da 337, daga cikinsu kuma 40 sun mutu, yayinda 255 suka warke.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana shirin sassautawa jama’a damar zirga-zirga a Jihohin Legas da Abuja da Ogun daga makon gobe, yayin da ya sanar da rufe Jihar Kano na makwanni biyu, matakin da jama’a ke tofa albarkacin bakinsu akai, kamar yadda za a ji cikin rahoton da da wakilimu daga Abuja, Muhammad Kabir Yusuf ya hada.

01:36

Buhari ya bada umarnin kulle Kano tsawon mako 2

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.