Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Kungiyar likitocin Najeriya ta bukaci Buhari ya tsawaita dokar kulle

Kungiyar likitocin Najeriya ta shawarci gwamnatin kasar da ta kara wa’adin dokar hana zirga-zirgar da ta kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus, wadda ta shafe makwanni 4 tana aiki a jihohin Legas Ogun da kuma birnin Abuja.

Wani sashin birnin Legas bayan kafa dokar hana zirga zirga domin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Wani sashin birnin Legas bayan kafa dokar hana zirga zirga domin dakile yaduwar annobar coronavirus. AFP
Talla

Cikin daren lahadin nan wa’adin dokar zai kare, inda ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayiwa ‘yan kasa karin bayani kan mataki na gaba.

Sai dai kungiyar likitocin kasar tace kamata yayi a kara wa’adin dokar kullen, la’akari da yadda a kullum adadin wadanda cutar ta coronavirus ke kamawa ke karuwa, gami da gaggauwar bazuwarta zuwa karin jihohin kasar da a yanzu yawansu ya kai 28.

Tuni dai shawarar kungiyar likitocin Najeriya ta haifar da ce-ce-kuce, inda gamayyar kungiyoyin kasuwanci, kamfanoni da masana’antu, da kuma na fannin hakar ma’adanai da noma, suka yi watsi da bukatar tsawaita dokar hana zirga-zirgar.

Gamayyar kungiyoyin sun ce a maimakon tsawaita hana fitar, kamata yayi gwamnatin Najeriya ta duba alherin bada damar cigaba da hada-hadar ayyuka da kasuwanni ko da ace ba kamar yadda lamarin yake a baya ba, domin kuwa hakan zai ceto tattalin arzikin kasar daga tagayyara, zalika jama’a za su samu saukin halin kuncin da suka shiga.

A karshen makon nan, kwamishinan lafiyar jihar Legas Farfesa Akin Aboyami, yayi gargadin cewa har yanzu annobar coronavirus bata kai koluluwar yaduwa ba a birnin.

Zalika a karshen watan maris kwamishinan lafiyar yayi gargadin cewa, yawan wadanda za su kamu da cutar ta COVID-19 a birnin na Legas ka iya kaiwa dubu 39, amma idan jama’a suka kiyaye cinkoso, adadin zai iya tsayawa a dubu 13 kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.