Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Yawan masu cutar corona a Najeriya ya zarta dubu 1 amma 208 sun warke

Yawan wadanda cutar coronavirus ta kama a Najeriya ya haura dubu 1, bayan samun karin mutane 114 da suka kamu da cutar a ranar Juma’a.

Wasu 'yan Najeriya a birnin Abuja, yayin karbar tallafin abinci saboda dokar hana zirga-zirga dake aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus. 3/4/2020.
Wasu 'yan Najeriya a birnin Abuja, yayin karbar tallafin abinci saboda dokar hana zirga-zirga dake aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus. 3/4/2020. REUTERS/Afollabi Sotunde
Talla

Cikin rahoton da ta saba wallafawa a kowace rana, cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, tace an samu karin mutanen da annobar ta harba a jihohin kasar guda 9, da suka hada da Legas, Abuja, Zamfara, Gombe, Kaduna, Ogun, Edo, Oyo, da kuma Sokoto.

Jihar Legas ke kan gaba wajen yawan sabbin wadanda da suka kamu da cutar ta coronavirus ko COVID-19 a Najeriya da adadin mutane 80, sai Gombe mai mutane 21, yayinda Abuja ke da mutane 5, sai kuma jihohin Zamfara, da Edo masu mutane bibbiyu. Kaduna, Sokoto, Ogun da kuma Oyo kuwa kowanne na da mutum guda da cutar ta harba.

Cibiyar dakile yaduwar cutukan Najeriya, ta ce zuwa karfe 11 da mintuna 50 na daren Juma’ar da ta gabata 24 ga watan Afrilu da muke, jimillar mutane dubu 1 da 95 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar, daga ciki kuma 208 sun warke, yayinda kuma adadin wadanda suka mutu ya kai mutane 32.

Har yanzu dai jihar Legas ke kan gaba wajen fama da yaduwar annobar, inda mutane 657 suka kamu, sai Abuja mai mutane 138, yayinda Kano ke biye da 73, sai kuma Ogun mai mutane 35 da suka kamu, yayinda Gombe ke biye da 30.

A Katsina, zuwa lokacin wannan wallafa mutane 21 aka tabbatar sun kamu da cutar, yayinda 20 suka kamu a Osun, 19 a Edo, 18 a Oyo, sai kuma Borno mai mutane 12.

Jihohin Kwara, da Akwa Ibom na da adadin mutane 11 da annobar ta kama kowannensu, yayinda 10 suka kamu a Kaduna, 8 a Bauchi, mutane 6 a Delta, sai Ekiti mai mutane 4, Ondo da Rivers kuma na da mutane 3 kowanne. A karshe jihohin Jigawa, Zamfara, Sokoto, Niger, Enugu da Abia na da mutane bibbiyu da suka kamu da COVID-19, yayinda aka samu guda-guda da suka kamu a Adamawa, Filato, Benue, da kuma Anambra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.