Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Karin mutane 91 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Hukumomin Najeriya sun sanar da samun karin mutane 91 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya sanya adadin wadanda cutar ta harba a kasar kai dubu 1, da 273, yayinda annobar ta kashe karin mutane 5

Wani jami'in kiwon lafiya a birnin Abuja dake Najeriya, yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus.
Wani jami'in kiwon lafiya a birnin Abuja dake Najeriya, yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus. AFP
Talla

Alkaluman hukumar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya sun nuna cewar, mutane 43 daga cikin wadanda suka kamun na a Jihar Lagos, sai Sokoto da mutane 8, ita kuwa Taraba da mutane 6.

Jihohin Kaduna da Gombe na da mutane 6 kowanne, sai mutane 5-5 a Jihohin Ondo da Edo da Rivers da Bauchi da Oyo da kuma Abuja, yayin da Oyo ke da mutane 3 da suka kamu, sai Osun mai 2, yayinda Akwa Ibom da Bayelsa da Ebonyi da kuma Kebbi dake da mutum guda-guda.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin dake fama da cutar, kuma a baya bayan nan gwamna Aminu Bello Masari yayi karin bayani kan halin da ake ciki dangane da annobar.

00:58

Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari kan annobar coronavirus

Nura Ado Suleiman

Yanzu haka dai wannan annoba ta coronavirus ta ratsa daukacin jihohin Najeriya, banda Yobe da Nasarawa da Kogi da kuma Cross Rivers.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.