Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP da APC sun yi musayar yawu kan 'Yan Sandan Najeriya

Manyan jam’iyyun siyasar Najeriya, wato APC da PDP sun yi musayar yawu game da sauya wa manyan Jami’an ‘Yan Sandan kasar garuruwan aiki gabanin zaben 2019 da za a gudanar a ranar 16 ga wannan wata na Fabairu.

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta nanata kudirinta na nuna kwarewa a yayin zaben 2019
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta nanata kudirinta na nuna kwarewa a yayin zaben 2019 TheTrentOnline
Talla

Rundunar ‘Yan Sandan kasar ta ayyana sabbin kwamishinonin ‘Yan Sanda a jihohin Lagos da Kano da Anambra da Kwara da Adamawa da Akwa Ibom da sauransu, yayin da Kwamishinonin Kaduna da Abuja da Borno da Yobe da Rivers da Ogun da Benue suka ci gaba da zama a jihohinsu.

Har ila yau, akwai masu rike da mukaman mataimakan Sufeta Janar da aka sauya wa wuraren aikinsu.

Sai dai tuni jam’iyyar PDP ta zargi cewa, sauya wa manyan jami’an ‘Yan Sandan wuraren aiki, wani yunkuri ne na yi wa ‘yan takarar jam’iyyar APC alfarma.

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ta bakin mashawarcinsa na musamman kan kafafen yada labarai, ya ce, gwamnatin APC ba ta shirya gudanar da sahihin zabe ba, yayin da ta bukace ta da ta daina shigar da harkar tsaro cikin siyasa.

Tuni APC ta mayar da martani, in da ta yi watsi da zarge-zargen cewa, ita ce ummul-haba’i’sin sauya wa jami’an garuruwan aiki gabanin zaben.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta nanata kudirinta na nuna kwarewa a yayin gudanar da zaben shugabancin kasar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.