Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Rundunar sojin Najeriya ta gano masu shirin yiwa zaben kasar zagon kasa

Babban Hafson sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi zargin wasu kungiyoyin cikin gida na hada kai da wasu daga kasashen waje domin yi wa zaben shugaban kasa zagon kasa.

Babban Hafsan Sojan Najeriya  Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai thenewsnigeria
Talla

Babban Hafson Sojin wanda ke bayyana haka lokacin wani taro da manyan kwamandodin sojin kasar da ya gudana a Abuja babban birnin Najeriyar, ya ce su na da bayanan asiri da ke tabbatar musu da zargin a wasu sassan kasar.

Janar Buratai ya gargadi irin wadannan mutane da su sauya matsayi kan mummunar aniyar ta su, domin suna hada kai da rundunar 'yan Sanda da sauran hukumomin tsaro domin ganin burin su bai cika ba.

Kwanaki 12 dai ya rage a gudanar da zaben kasar wanda ke cike da kalubale musamman tsakanin jam'iyya mai mulki ta APC da ke fatan zarcewa da kuma babbar Jam'iyyar adawa ta PDP da ke neman mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.