Isa ga babban shafi
Najeriya

Ko kun san yadda Atiku ya shiga Amurka

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu damar ziyartar Amurka ne makwanni biyu da suka shude bayan mahukuntan kasar sun dage masa haramcin ba shi Bisa na wucen-gadi kamar yadda Kamfanin Dillanci Labarai na Reuters ya rawaito.

Tsohon shugaban Najeriya, Atiku Abubakar
Tsohon shugaban Najeriya, Atiku Abubakar REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Amurka ta soke bai wa Atiku Bisa ne saboda zargin sa da aikata laifin cin hanci da rashawa, yayin da majiyoyi ke cewa, an ba shi damar shiga kasar ne bayan wasu ‘yan siyasa sun nema masa alfarma daga wurin ‘yan Majalisar Dokokin Kasar.

‘Yan neman alfarmar sun fake da cewa, bai kamata gwamnatin Amurka ta yi watsi da babban dan takarar da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari ba a zaben watan Fabairu na 2019.

Wata majiya ta shaida wa Reuters cewa, Amurka ta bude wa Atiku kofa ne saboda gudun tabarbarewar alaka da shi da zaran ya samu nasara a zaben shugabancin Najeriya wadda ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Rotanni na cewa, Atiku ne ya dauki nauyin ‘yan siyasar da suka nema masa alfarma a wurin ‘Yan
Majalisar Amurka har suka shawo kan Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar game da ziyarar tasa.

Batun hana Atiku Bisa ya samo asali ne bayan zargin sa da karbar na goro daga wani wakilin Amurka, William Jefferson da zummar fadada harkar fasaha a Najeriya.

Tun a shekarar a shekarar 2009 aka tuhumi Jefferson a Amurka tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari. Koda yake daga bisani an rage masa tsawon shekarun zama gidan yarin.

Kazalika Amurka ta zargi cewa, daya daga cikin matan Atiku hudu, ta taimaka masa wajen tura sama da Dala miliyan 40 zuwa Amurka, (kudaden da aka diga ayar tambaya akan su) kuma ana zargin cewa, akalla Dala 1.7 daga cikinsu, ya karba ne a matsayin cin hanci daga wani kamfanin Siemens na Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.