Isa ga babban shafi
Najeriya

Fadar shugaban Najeriya za ta yi bincike kan faduwar jirgin Osinbajo

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce za ta yi kwakkwaran bincike game da faduwar jirgin mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo a Kabba na jihar Kogi, a ci gaba da ziyarce-ziyarcensa na neman goyon bayan al’umma kan takarar sake shugabancin kasar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi.

Rahotanni sun ce babu wanda ya yi rauni a hadarin jirgin na mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Rahotanni sun ce babu wanda ya yi rauni a hadarin jirgin na mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo News Agency of Nigeria (NAN)
Talla

Babban mataimaki na musamman ga Farfesa Osinbajo, Mr Laoulu Akande yayin ganawarsa da manema labarai kan batun, ya ce tabbas za a gudanar da kwakkwaran bincike don sanin abin da ya haddasa faduwar jirgin.

Laolu Akande ya ce Osinbajo da tawagarsa na cikin koshin lafiya babu wanda ya samu rauni a hadarin, inda bayan afkuwar hadarin ma kai tsaye ya ci gaba da ziyarsa ta neman hadin kan al’umma dai dai lokacin da babban zaben kasar ya rage kasa da mako biyu.

A nata bangaren babbar jam’iyyar adawa ta Najeriyar PDP, ta mika sakon fatan alkhairi da mataimakin shugaban ya tsira da raywarsa yayinda ta bukaci gudanar da bincike kan batun.

A bangare guda ita ma Jam’iyya mai mulki cikin sanarwar da ta fitar ta yi sam barka da yadda tawagar mataimakin shugaban ta tsira a hadarin, yayin da ta yi fatan alkhairi a gangamin yakin neman zaben sake hawa kujerar mulkin Najeriyar da mambobinta ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.