Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai hukunta ma'aikata kan wanko kalaman Obama

Fadar gwamnatin Najeriya za ta hukunta ma’aikatanta da suka wanko kalaman shugaban Amurka Barack Obama, inda suka sanya su a cikin jawaban da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a lokacin kaddamar da shirin “gyra halinka” mai taken sauyi ya fara daga kaina.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka, Barack Obama
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar ta ce, tuni wani matamakin Direkta ya amsa laifin shigar da kalaman, wadanda suka haifar da cece-kuce a Najeriya.

Sanawar ta kara da cewa, fadar ta yi da-na-sanin abin da ya faru tare da yin alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba nan gaba.

Shugaba Buhari dai ya bukaci ‘yan Najeriya da su mayar da hanlaki kan muhimmacin shirin a maimakon ci gaba da cece-kuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.