Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bayar da umarnin kama makusancinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kama wani makusancinsa kuma jigo a kwamitin da ke bincike kan badakalar siyan makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

Le président du Nigeria, Muhammadu Buhari, le 11 juin 2015 lors de l'ouverture du sommet d'Abuja.
Le président du Nigeria, Muhammadu Buhari, le 11 juin 2015 lors de l'ouverture du sommet d'Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari ya bayar da umarnin ne bayan ya samu rahotannin da ke cewa, ana zargin Mohammed Umar mai ritaya da karban cin hanci da rashawa tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

A makon jiya ne aka kama Umar bayan jami’an hukumar tsaron farin kaya wato SSS sun kai masa samame a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Gabanin kama shi, sai da Darekta Janar na hukumar ta SSS, Lawal Daura ya gana da Buhari, inda ya shaida masa cewa Mr. Umar na amfani da sunan shugaban kasa wato Buhari da wasu manyan jami’an gwamnati wajen karban kudade daga hannun mutane da suka hada da ‘yan kasuwa bayan ya razana su.

Wannan lamarin dai ya tayar da hankalin shugaba Buhari, ganin cewa mutumin da ya amincewa ne ke aikata wannan kazamin aikin kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.

Mohammed Umar dai ya yi ritaya ne daga aikin sojin sama a matsayin mai rike da mukamin Air Commodore a cikin watan Janairun shekara ta 2014, yayin da hukumomin kasar suka ce, ya mallaki kamfanoni guda shida da suka hada da wani kamfani da ke harkar jiragen sama na musamman.

Wata majiyar tsaro ta ce, Umar na daga cikin attajiran da ke sahun gaba wajen mallakar kadarori a Abuja.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.