Isa ga babban shafi
Najeriya

Yunwa na kashe 'yan gudun hijira a Borno

A Najeriya yanzu haka ana ci gaba da samun rahotanni da ke tabbatar da cewa mutane da dama ne ke rasa rayukansu a kowace rana sakamakon karancin abinci a cikin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jiyar Borno.

Yunwa na ci gaba da kashe 'yan gudun hijirar Boko Haram a Borno
Yunwa na ci gaba da kashe 'yan gudun hijirar Boko Haram a Borno REUTERS/Albert Gonzalez Farran
Talla

Ko a makon jiya, kungiyar likitoci mai zaman kanta, MSF ta ce sama da mutane 200 ne suka rasa rayukansu a cikin wata guda a wasu sansanoni da ke Bama.

A baya can, gwamnatin jihar Borno da kungiyoyin agaji na duniya sun yi gargadi dangane da tsananin karancin abinci a sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci a gudanar da bincike don yi masa bayani kan wannan rahoton  yunwar da aka fitar.

Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa game da rahoton da ya bayyana matsalar da ta cika da ‘yan gudun hijirar duk da biliyoyin Naira da kayayyaki da gwamnatin Najeriya ta ware domin kyautata wa ‘yan gudun hijirar na Boko Haram.

Sannan kuma ga tallafin da gwamnatin jihar Borno ke bayarwa, baya ga kungiyoyin agaji daban daban da kuma dai- dai-kum mutanen da ke bayar da taimakonsu amma duk da haka aka samu wannan rahoton.

A game da wannan batu, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tuntubi  mai magana da yawun hukumar bayar da agaji ta Najeriya, NEMA, wato Sani Datti.

03:21

Sani Datti na NEMA kan yunwa a sansanin 'yan hijira

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.