Isa ga babban shafi
Nijar

Rundunar hadaka ta fara aikin kakkabe Boko Haram

Rundunar sojin jamhuriyar Nijar ta baynanna cewa, rundunar hadakar kasashe ta fara aikin kakkabe kungiyar Boko Haram a kan iyakar kasar da Najeriya.

Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi za su yi wa Boko Haram taron dangi
Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi za su yi wa Boko Haram taron dangi AFP PHOTO / ALI KAYA
Talla

Shugaban tsare tsare na sojin da aka girke a yankin Diffa, Birgediya Janar Abdou Sidikou Issa ya sanar da haka a jiya Talata.

Janar Issa ya kara da cewa, sojojin Najeriya da Chadi na cikin rundunar domin yi wa mayakan na Boko Haram taron dangi.

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kaddamar da hare hare a wadannan kasashen, inda suka hallaka jama’a da dama tare da tilasta wa wasu kaurace wa gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.