Isa ga babban shafi
Nijar

Dakarun Chadi sun isa Nijar

Chadi ta tura sojoji dubu biyu zuwa jamhuriyar Nijar, kwana daya bayan da shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya gana da Idris Deby a birnin N’Djamena, inda bayanai ke nuni da cewa shugaban ya je neman taimakon Chadi ne domin fada da ‘yan Boko Haram.

Sojin Nijar sun kwato garin Bosso daga hannun mayakan Boko Haram
Sojin Nijar sun kwato garin Bosso daga hannun mayakan Boko Haram RFI/Madjiasra Nako
Talla

Shaidu sun ce sojojin kasar ta Chadi na dauke da ne manyan makamai, kuma bisa ga dukkan alamu sun nufi yankin Bosso ne inda ‘yan Boko Haram suka kai a hari tare da kashe sojin Nijar 26 a makon jiya.

Wata majiyar tsaro tace dakarun Chadi 30 sun isa yankin Bosso a Nijar

Yanzu haka dubban mutane ne ke rayuwa a cikin hali na rashin abinci da matsuguni, bayan sun tsere daga Bosso.

Majalalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 50,000 suka fice daga Bosso tun lokacin da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.