Isa ga babban shafi
Boko Haram

Nijar za ta yaki Boko Haram

Nijar ta sha alwashin murkushe mayakan Boko Haram bayan kashe sojojin kasar 26 a wani mummunan harin da mayakan suka kai a garin Bosso da ke kan iyaka da Najeriya.

Sojojin Nijar da ke fada da Mayakan Boko Haram a yankin Bosso
Sojojin Nijar da ke fada da Mayakan Boko Haram a yankin Bosso ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ministan tsaro Hassoumi Massoudou ya ce za su ci gaba da yaki domin daukar fansa.

Rahotanni sun ce mayakan Boko Haram sun karbe ikon garin na Bosso ranar Lahadi, bayan kwashe dogon lokaci suna dauki ba dadi da Jami’an tsaron Nijar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato Magajin Garin Bosso na tabbatar da kama garin a ranar Litinin.

Amma Ma’aikatar tsaron Nijar tace dakarunta sun kwato garin.

Baya ga kashe Sojojin Nijar 26 da wasu na Najeriya 2, mayakan Boko Haram sun kuma lalata motocin Sojin tare da kone gidajen mutane.

Sannan kimanin Sojoji 67 suka samu rauni, amma an kashe ‘Yan Boko Haram 55 tare da jikkata wasu da dama.

Moussa Aksar wani mazaunin Yankin Bosso ya shaidawa RFI Hausa cewa mutane da dama sun fice daga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.