Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutanen Tafkin Chadi Miliyan 9 na bukatar Tallafin abinci

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane miliyan 9 a tafkin Chadi na bukatar tallafin abinci, yankin da rikicin Boko Haram ya daidaita tare da raba miliyoya da muhallinsu.

Sama da mutane miliyan biyu da rabi rikicin Boko Haram ya tursasawa kauracewa gidajensu a Tafkin Chadi
Sama da mutane miliyan biyu da rabi rikicin Boko Haram ya tursasawa kauracewa gidajensu a Tafkin Chadi RFI/Sayouba Traoré
Talla

Ofishin da ke kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya yace kusan rabin mutanen yankin na fama da matsalar karancin abinci a yayin da kuma suke ci gaba da fuskantar barazanar hare haren ‘yan Boko Haram.

Sama da mutane miliyan biyu da rabi rikicin Boko Haram ya tursasawa kauracewa gidajensu, a cewar rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.

Rundunar hadin guiwa da aka kafa tsakanin dakarun da ke kewaye da tafkin Chadi, Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ya taimaka wajen karya lagon ‘Yan Boko Haram, amma har yanzu mayakan na barazana ga rayukan mutanen yankin.

Yanzu haka babban Jami’in kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya fara ziyarar kwanaki hudu domin ganin halin da mutanen yankin ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.