Isa ga babban shafi
Boko Haram

Amurka za ta tallafawa kasashen Tafkin Chadi

Gwamnatin Amurka ta yi alkawarin tallafawa kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa kusa da tafkin Chadi da kudaden da suka kai Dala miliyan 40. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta sanar da haka tare da cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen tallafawa mutane kusan miliyan 7 da rikicin ya shafa.

Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power.
Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power. REUTERS/Amir Cohen
Talla

Power ta sanar da haka ne bayan ganawa da shugaba Paul Biya a Kamaru kafin ta isa kasashen Chadi da Najeriya.

Sannan ta kara da cewa adadin taimakon da Amurka ta bai wa Yankin yanzu haka ya kai Dala miliyan 237.

Jekadiyar ta Amurka ta ta kai ziyarar ne a Kamaru tare da rakiyar Jami’an tsaron Amurka da hukumar agaji ta USAID domin tattaunawa da mahukuntan kasar kan tallafin Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.